>

Abubakar Mahmoud Gumi — 446

37:1 Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).

37:2 Sa'an nan mãsu yin tsãwa[1] dõmin gargaɗi.

37:3 Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.

37:4 Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.

37:5 Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.

37:6 Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.

37:7 Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.

37:8 Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.

37:9 Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.

37:10 Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.

37:11 Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.

37:12 Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.

37:13 Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.

37:14 Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.

37:15 Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."

37:16 "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?

37:17 "Ashe kõ da ubanninmu na farko?"

37:18 Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."

37:19 Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.

37:20 Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."

37:21 Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.

37:22 Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.

37:23 Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.

37:24 Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.