Abubakar Mahmoud Gumi — 445
36:71 Shin, ba su gani ba (cẽwa) lalle Mun halitta musu dabbõbi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai sunã mallakar su?
36:72 Kuma Muka hõre su, sabõda su, sabõda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci.
36:73 Kuma sunã da waɗansu amfãnõni a cikinsu, da abũbuwan shã. Ashe fa, bã zã; su gõdẽ ba?
36:74 Kuma suka riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa wanin Allah, ɗammãninsu zã su taimake su.
36:75 Bã zã su iya taimakonsu ba, alhãli kuwa sũ runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wutã).
36:76 Sabõda haka, kada maganarsu ta ɓãta maka rai. Lalle Mũ, Munã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa.
36:77 Ashe, kuma mutum bai ga (cẽwa) lalle Mũ, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai gã shi mai yawan husũma, mai bayyanãwar husũmar.
36:78 Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu?"
36:79 Ka ce: "Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne."
36:80 "Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi."
36:81 "Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne, Mai ilmi."
36:82 UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).
36:83 Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.