Abubakar Mahmoud Gumi — 444
36:55 Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi.
36:56 Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira.
36:57 Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo.
36:58 "Aminci," da magana,[1] daga Ubangiji Mai jin ƙai.
36:59 "Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!"
36:60 "Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?"
36:61 "Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya."
36:62 "Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba?"
36:63 "Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita."
36:64 "Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."
36:65 A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
36:66 Dã Mun so, dã Mun shãfe gani [1]daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani?
36:67 Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba.
36:68 Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta?
36:69 Ba Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne.
36:70 Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai.