>

Abubakar Mahmoud Gumi — 440

35:45 Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne sabõda abin da suka aikata, dã bai bar wata dabba ba a kanta (kasã). Amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambatã. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, to, lalle Allah yã kasance Mai gani ga bãyin Sa.

36:1 Y. S̃.

36:2 Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni[1] Mai hikima.

36:3 Lalle kai, haƙĩƙa kanã cikin Manzanni.

36:4 A kan hanya madaidaiciya.

36:5 (Allah Ya saukar da Al-kur'ãni) saukarwar Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

36:6 Dõmin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutãne da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, sabõda haka sũmasu rafkana ne.

36:7 Lalle, haƙĩƙa, kalma[1] tã wajaba a kan mafi yawansu, dõmin sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.

36:8 Lalle Mũ, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyõyinsu, sa'an nan sũ (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓõɓinsu, sabõda haka, sũ banƙararru ne.

36:9 Kuma Muka sanya wata tõshiya a gaba gare su, da wata tõshiya a bãyansu, sabõda haka Muka rufe su, sai suka zama bã su gani.

36:10 Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, sũ bã zã su yi ĩmãni ba.

36:11 Kanã yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ãni ne, kuma ya ji tsõron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushãra da gãfara da wani sakamako na karimci.

36:12 Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da matattu kuma Mu rubũta abin da suka gabãtar, da gurãbunsu, kuma kõwane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littãfi Mabayyani.