>

Abubakar Mahmoud Gumi — 437

35:19 Kuma makãho bã ya daidaita da mai gani.

35:20 Kuma duffai bã su daidaita, kuma haske bã ya daidaita.

35:21 Kuma inuwa bã ta daidaita, kuma iskar zãfi bã ta daidaita.

35:22 Kuma rãyayyu bã su daidaita kuma matattu ba su daidaita. Lalle Allah Yanã jiyar da wa'azi ga wanda Ya so, kuma ba ka jiyar da waɗanda suke a cikin kaburbura.

35:23 Ba ka zama ba fãce mai gargaɗi kawai.

35:24 Lalle Mũ Mun aike ka da gaskiya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Kuma bãbu wata al'umma fãce wani mai gargaɗi yã shũɗe a cikinta.

35:25 Kuma idan sunã ƙaryata ka, to, haƙĩƙa, waɗanda suke a gabãninsu sun ƙaryata. Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji, kuma da takardu, kuma da Littafi mai haske.

35:26 Sa'an nan Na kãma waɗanda suka kãfirta. To, yãya musũ Na yake?

35:27 Ba ka gani ba, lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama? Sai Muka fitar, game da shi,'yã'yan itãce mãsu sãɓanin launuka kuma daga duwatsu akwai zane-zane, farfaru da jãjãye, mãsu sãɓanin launin, da mãsu launin baƙin ƙarfe, baƙãƙe.

35:28 Kuma daga mutãne da dabbõbi da bisãshen gida, mãsu sãɓãnin launinsu kamar wancan. Malamai kawai ke tsõron Allah daga cikin bãyin Sa. Lalle, Allah, Mabuwãyi ne, Mai gãfara.

35:29 Lalle waɗanda ke karãtun Littãfin Allah[1] kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sunã fãtan (sãmun) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro.

35:30 Dõmin (Allah) zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙarã musu daga falalarSa. Lalle Shi Mai gãfara ne, Mai gõdiya.