>

Abubakar Mahmoud Gumi — 431

34:23 "Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurin Sa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye[1] tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma,"

34:24 Ka ce: "Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?" Ka ce: "Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya."

34:25 Ka ce: "Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba."

34:26 Ka ce: "Ubangijinmu zai tãra tsakãninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani."

34:27 Ka ce: "Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima."

34:28 Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.

34:29 Sunã cẽwa, "Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance mãsu gaskiya?"

34:30 Ka ce: "Kunã da mi'ãdin wani yini wanda bã ku jinkirta daga gare shi kõ da sa'a ɗaya, kuma bã ku gabãta."

34:31 Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba, kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba (na waɗansu littattafan sama)." Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa makangara (shũgabanni) "Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai."