>

Abubakar Mahmoud Gumi — 415

32:1 A. L̃. M̃.

32:2 Saukar da Littafin bãbu shakka a gare shi, daga Ubangijin tãlikai yake.

32:3 Kõ sunã cẽwa (Muhammadu ne) ya ƙirƙira shi? Ã'a, shĩ ne gaskiya daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda wani mai gargaɗi bai je musu ba a gabãninka, fãtan zã su shiryu.

32:4 Allah ne wanda Ya halitta sammai da ƙassai da abin da yake a tsakãninsu a cikin kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Bã ku da, baicin Shi, wani majiɓinci kuma babu wani maceci. Shin, bã zã ku yi tunãni ba?

32:5 Yanã shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasã, sa'an nan ya tãka zuwa gare Shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shẽkaru dubu ne ga abin da kuke lissafãwa.

32:6 Wannan shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwãyi, Mai jinƙai.

32:7 Wanda Ya kyautata kõme, Wanda Ya halitta shi. Shi ne kuma Ya fãra halittar mutum daga lãka.

32:8 Sa'an nan Ya sanya ɗiyansa daga wani asali na wani ruwa wulãkantacce.

32:9 Sa'an nan Ya daidaita shi, kuma Ya hũra a cikinsa, daga ruhinSa kuma Ya sanya muku ji, da ganunuwa da zukãta. Gõdiyarku kaɗan ce ƙwarai.

32:10 Kuma suka ce: "Shin, idan mun ɓace a cikin ƙasã, shin, lalle mu, tabbas ne munã zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Ã'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kãfirai

32:11 Ka ce: "Mala, ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shĩ ne ke karɓar rãyukanku.[1] Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku."