>

Abubakar Mahmoud Gumi — 411

31:1 A. L̃. M̃.

31:2 Waɗancan ãyõyin Littãfin ne mai hikima.

31:3 Shiriya da rahama ne ga mãsu kyautatawa.

31:4 Waɗanda ke tsai da salla kuma sunã bãyar da zakka kuma sũ, sunã yin ĩmãnin yaƙĩni, ga lãhira.

31:5 Waɗannan sunã a kan shiriya ta daga Ubangijinsu kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.

31:6 Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi[1] dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa.

31:7 Kuma idan an karanta ãyõyin Mu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai, kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi.

31:8 Lalle, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljannar ni'ima.

31:9 Sunã dawwama a cikinsu Allah Yã yi alkawarin, Ya tabbatar da shi. Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.

31:10 (Allah) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa.

31:11 Wannan shĩ ne halittar Allah. To ku nũna mini, "Mẽne ne waɗanan da ba Shi ba suka halitta? Ã'a, azzalumai sunã a cikin ɓata bayyananna."