Abubakar Mahmoud Gumi — 406
30:16 Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba.
30:17 Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da lõkacin da kuke shiga sãfiya.[1]
30:18 Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin zawãli.
30:19 Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku.
30:20 Kuma akwai daga ãyõyin Sa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum, kunã wãtsuwa.
30:21 Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku.[1] Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.
30:22 Kuma akwai daga ãyõyin Sa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi.
30:23 Kuma akwai daga cikin ãyõyin Sa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa.
30:24 Kuma akwai daga cikin ãyõyin Sa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa.