>

Abubakar Mahmoud Gumi — 39

2:238 Ku tsare[1] lõkatai a kan sallõli da salla mafificiya. Kuma ku tsayu kuna mãsu ƙanƙan da kai ga Allah.

2:239 To, idan kun ji tsõro, to (ku dai yi salla gwargwadon hali) da tafiya ƙasa kõ kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince sai ku ambaci Allah, kamar yadda Ya nũna muku abin da ba ku kasance kuna sani ba.

2:240 Kuma waɗanda suke mutuwa[1] daga gare ku, alhãli suna barin mãtan aure, wasiyya ga mãtan aurensu da dãɗaɗãwa zuwa ga shekara guda bãbu fitarwa, to, idan sun fita to bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.

2:241 Kuma waɗanda aka saki suna da dãɗaɗãwa gwargwadon hãli, wajibi ce a kan mãsu jin tsoron Allah[1] .

2:242 Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa; tsammãninku, kuna hankalta.

2:243 Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita[1] daga gidãjensu, alhãli kuwa sũ dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu." Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, haƙĩƙa Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa.

2:244 Kuma ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mai jĩ ne, Masani.

2:245 Wãne ne wanda[1] zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya riɓanya masa, riɓanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku.