>

Abubakar Mahmoud Gumi — 376

26:207 Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare[1] su.

26:208 Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi.

26:209 Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba.

26:210 Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba.

26:211 Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa.

26:212 Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne.

26:213 Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba.

26:214 Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci.

26:215 Kuma ka sassauta fikãfikanka[1] ga wanda ya bĩ ka daga mũminai.

26:216 Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa."

26:217 Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

26:218 Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye.

26:219 Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada.

26:220 Lalle Shi, Shi[1] ne Mai ji, Masani.

26:221 Shin, (kunã so) in gaya[1] muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?

26:222 Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi.

26:223 Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne.

26:224 Kuma mawãƙa[1] halakakku ne ke bin su.

26:225 Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba?

26:226 Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa?

26:227 Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa.