>

Abubakar Mahmoud Gumi — 375

26:184 "Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko."

26:185 Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne."

26:186 "Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata."

26:187 "To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya."

26:188 Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa."

26:189 Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije[1] ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.

26:190 Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

26:191 Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

26:192 Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne.

26:193 Rũhi[1] amintacce ne ya sauka da shi.

26:194 A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi.

26:195 Da harshe na Larabci mai bayãni.

26:196 Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko.

26:197 Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi?

26:198 Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa,

26:199 Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba.

26:200 Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.

26:201 Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi.

26:202 Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba.

26:203 Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?"

26:204 Ashe, to, da azãbar Mu suke nẽman gaggãwa?

26:205 Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru,

26:206 Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu,