Abubakar Mahmoud Gumi — 374
26:160 Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni.
26:161 A lõkacin da ɗan'uwansu,[1] Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
26:162 "Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce."
26:163 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
26:164 "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
26:165 "Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"
26:166 "Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"
26:167 Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."
26:168 Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."
26:169 "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."
26:170 Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya.
26:171 Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa.
26:172 Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu.
26:173 Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.
26:174 Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba.
26:175 Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
26:176 Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni.
26:177 A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
26:178 "Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce."
26:179 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã."
26:180 "Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
26:181 "Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)."
26:182 "Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce."
26:183 "Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna."