>

Abubakar Mahmoud Gumi — 373

26:137 "Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen[1] mutãnen farko."

26:138 "Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba."

26:139 Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

26:140 Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

26:141 Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni.

26:142 A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?"

26:143 "Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce."

26:144 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.

26:145 "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu."

26:146 "Shin, anã barin ku[1] a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?"

26:147 "A cikin gõnaki da marẽmari."

26:148 "Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi[1] mãsu narkẽwa a ciki?"

26:149 "Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?"

26:150 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

26:151 "Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata."

26:152 "Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa."

26:153 Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake."

26:154 "Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya."

26:155 Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan[1] yini, kuma kunã da shan yini sasanne."

26:156 "Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku."

26:157 Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma.

26:158 Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

26:159 Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai.