Abubakar Mahmoud Gumi — 372
26:112 Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."
26:113 "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."
26:114 "Ban zama mai kõre mũminai ba."
26:115 "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."
26:116 Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"
26:117 Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."
26:118 "Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai."
26:119 Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.
26:120 Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.
26:121 Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
26:122 Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.
26:123 Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni.
26:124 A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
26:125 "Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce."
26:126 "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
26:127 "Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu."
26:128 "Shin, kunã yin ginin sitadiyo[1] a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?"
26:129 "Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?[1]"
26:130 "Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa."
26:131 "To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
26:132 "Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani."
26:133 "Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya."
26:134 "Da gõnaki da marẽmari."
26:135 "Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma."
26:136 Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba."