>

Abubakar Mahmoud Gumi — 371

26:84 "Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya[1] a cikin mutãnen ƙarshe."

26:85 "Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima."

26:86 "Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu."

26:87 "Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su."

26:88 "A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi."

26:89 "Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."

26:90 Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.

26:91 Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.

26:92 Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?"

26:93 "Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?"

26:94 Sai aka kikkife su[1] a cikinta, su da halakakkun.

26:95 Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.

26:96 Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,

26:97 "Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna."

26:98 "A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu.

26:99 "Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi."

26:100 "Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta."

26:101 "Kuma bã mu da abõki, masõyi."

26:102 "Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!"

26:103 Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.

26:104 Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

26:105 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.

26:106 A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba?"

26:107 "Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce."

26:108 "To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

26:109 "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."

26:110 "Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."

26:111 Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?"