>

Abubakar Mahmoud Gumi — 370

26:61 Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne."

26:62 Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."

26:63 Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge,[1] kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.

26:64 Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.

26:65 Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.

26:66 Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.

26:67 Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.

26:68 Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.

26:69 Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.

26:70 A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?"

26:71 Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su."

26:72 Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?"

26:73 "Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?"

26:74 Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa."

26:75 Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?"

26:76 "Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?"

26:77 "To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu."

26:78 "Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni."

26:79 "Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni."

26:80 "Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni."

26:81 "Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni."

26:82 "Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako."

26:83 "Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."