Abubakar Mahmoud Gumi — 369
26:40 "Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya."
26:41 To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?"
26:42 Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai."
26:43 Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa."
26:44 Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya."
26:45 Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.
26:46 Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.
26:47 Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta."
26:48 "Ubangijin Mũsa da Hãrũna."
26:49 Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya."
26:50 Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu."
26:51 "Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni."
26:52 Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã[1] ne.
26:53 Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.
26:54 "Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan."
26:55 "Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne."
26:56 "Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne."
26:57 Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.
26:58 Da taskõki da mazauni mai kyau.
26:59 Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.
26:60 Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.