>

Abubakar Mahmoud Gumi — 368

26:20 Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi."

26:21 "Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."

26:22 "Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."

26:23 Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"

26:24 Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni."

26:25 Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"

26:26 Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."

26:27 Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."

26:28 Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta."

26:29 Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru."

26:30 Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"

26:31 Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya."

26:32 Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.

26:33 Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.

26:34 (Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi!

26:35 "Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?"

26:36 Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne."

26:37 "Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani."

26:38 Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.

26:39 Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne?