Abubakar Mahmoud Gumi — 367
26:1 T. S̃. M̃.
26:2 Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
26:3 Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba! [1]
26:4 Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
26:5 Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
26:6 To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.
26:7 Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?
26:8 Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.
26:9 Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
26:10 Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.
26:11 "Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"
26:12 Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.
26:13 "Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci[1] kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.
26:14 "Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."
26:15 Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."
26:16 "Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne."
26:17 "Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."
26:18 Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"
26:19 "Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"