>

Abubakar Mahmoud Gumi — 364

25:44 Ko kanã zaton cẽwa mafi yawansu sunã ji, kõ kuwa sunã hankali? sũ ba su zama ba fãce dabbõbin gida[1] suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa ga hanya.

25:45 Ashe, ba ka dũba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma dã Yã so dã Yã bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rãnã mai nũni a kanta.

25:46 Sa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi.

25:47 Kuma shĩ ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tũfa da barci ya zama hũtãwa, dã yini ya zama lokacin tãshi (kamar Tashin ¡iyãma).

25:48 Kuma Shi ne Ya aika iskõkin bushãra gaba ga rahamar Sa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakẽwa daga sama.

25:49 Dõmin Mu rãyar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbõbi da mutãne mãsu yawa daga abin da Muka halitta.

25:50 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sarrafa[1] shi (Alƙur'ãni) a tsakãninsu, dõmin su yi tunãni, sai dai mafi yawan mutãnen sun ƙi fãce kãfirci.

25:51 Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi[1] a ciƙin kõwace alƙarya.

25:52 Sabõda haka kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai, ka yãke su, da shi, yãƙi mai girma.

25:53 Kuma shĩ ne Ya gauwaya tẽkuna biyu, wannan mai dãdi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurbatacce, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãninsu da kãriya mai shãmakacẽwa.

25:54 Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ĩkon yi.

25:55 Kuma sunã bauta wa, baicin Allah, abin da bã ya amfãnin su, kuma bã ya cũtar su, kuma kãfiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa.