Abubakar Mahmoud Gumi — 363
25:33 Kuma bã zã su zo maka da wani misãli ba, fãce Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara.
25:34 Waɗanda ake tãyarwa a kan fuskõkinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan sũ ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacẽwa ga hanya.
25:35 Kuma lalle ne, Mun bai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Hãrũna, mataimaki tãre da shi.
25:36 Sai Muka ce: "Ku tafi, kũ biyu, zuwa ga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata game da ãyõ yin Mu." sai Muka darkãke su, darkãkewa.
25:37 Kuma mutãnen Nũhu, a lõkacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata ãya ga mutãne, kuma Muka yi tattalin azãba mai raɗaɗi ga azzãlumai.
25:38 Da Ãdãwa da Samũdãwa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakãnin wannan, mãsu yawa.
25:39 Kuma kõwannensu Mun buga masa misãlai, kuma kõwanne Mun halakar da (shi), halakarwa.
25:40 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, (¡uraishi) sun jẽ a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azãba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? Ã'a, sun kasance bã su ƙaunar tãyarwa (a ¡iyãma).
25:41 Kuma idan sun gan ka, bã su rikon ka fãce da izgili, (sunã cẽwa) "Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo?
25:42 "Lalle ne, yã yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in bã dõmin da muka yi haƙuri a kansu ba."Kuma zã su sani a lõkacin da suke ganin azãba, wãne ne mafi ɓacẽwa ga hanya!
25:43 Shin, kã ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancẽwa mai tsaro a kansa?