>

Abubakar Mahmoud Gumi — 347

23:75 Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa.

23:76 Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba[1] sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u.

23:77 Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi.[1]

23:78 Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa.

23:79 Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku.

23:80 Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba?

23:81 Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa.

23:82 Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lale ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne?

23:83 "Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko."

23:84 Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani?"

23:85 Zã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba?"

23:86 Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma?"

23:87 Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba?"

23:88 Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani?"

23:89 Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku?"