>

Abubakar Mahmoud Gumi — 344

23:28 "Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai."

23:29 "Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.'"

23:30 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙiƙa' Mãsu jarrabãwa.

23:31 Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu.

23:32 Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba?"

23:33 Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã."

23:34 "Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne."

23:35 "Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da kasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne?"

23:36 "Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi."

23:37 "Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa,[1] kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."

23:38 "Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba."

23:39 Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni."

23:40 Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma."

23:41 Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai!

23:42 Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu.