Abubakar Mahmoud Gumi — 330
21:91 Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu.[1] Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.
21:92 Lalle ne wannan[1] ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini.
21:93 Kuma suka kakkãtse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni
21:94 Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne.
21:95 Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa.
21:96 Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa.
21:97 Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!"
21:98 (A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin[1] da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."
21:99 Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne.
21:100 Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme.
21:101 Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne.