>

Abubakar Mahmoud Gumi — 327

21:58 Sai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi.

21:59 Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai."

21:60 Suka ce: "Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm."

21:61 Suka ce: "To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida."

21:62 Suka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!"

21:63 Ya ce: "Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana."

21:64 Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: "Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai."

21:65 Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana."

21:66 Ya ce: "Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah?"

21:67 "Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta?"

21:68 Suka ce: "Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa."

21:69 Muka ce: "Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm."

21:70 Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra.

21:71 Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai.

21:72 Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai.