Abubakar Mahmoud Gumi — 326
21:45 Ka ce: "Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi," kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi.
21:46 Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cẽwa, "Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci."
21:47 Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi.
21:48 Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa.
21:49 Waɗanda suke tsãron Ubangijinsu a fake, alhãli kuwa sũ, mãsu sauna ne daga Sa'a.
21:50 Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi?
21:51 Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi.
21:52 Ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu?"
21:53 Suka ce: "Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu."
21:54 Ya ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananne."
21:55 Suka ce: "Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãsu wãsã ne?"
21:56 Ya ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka."
21:57 "Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya."