Abubakar Mahmoud Gumi — 323
21:11 Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta.
21:12 Sai a lõkacin da suka hangi azãbar Mu, sai gã su sunã gudu daga gare ta.
21:13 "Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku."
21:14 Suka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci."
21:15 Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu.
21:16 Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba.
21:17 Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun[1] riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa.
21:18 Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa.
21:19 Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurin Sa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdar Sa. kuma bã su gajiya.
21:20 Sunã tasbĩhi dare da rãnã, bã su yin rauni.
21:21 Kõ (kãfirai) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa ne ga ƙasã, su ne mãsu tãyarwa (gare su)?
21:22 Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa.
21:23 Bã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su.
21:24 Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: "Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne."