>

Abubakar Mahmoud Gumi — 321

20:126 Ya ce: "Kamar wancan ne ãyõyin Mu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka."

20:127 Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita,[1] kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa

20:128 Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda (kãfirai) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula.

20:129 Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta.

20:130 Sai ka yi haƙuri[1] a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda.

20:131 Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikin sa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa.

20:132 Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani Arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa.

20:133 Kuma suka ce: "Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa?" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba?

20:134 Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: "Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu!"

20:135 Ka ce: "Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa."