Abubakar Mahmoud Gumi — 32
2:203 Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙidayayyu.[1] To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma ku sani cewa lalle ne kũ, zuwa gare Shi ake tãrã ku.
2:204 Kuma akwai daga mutãne[1] wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne.
2:205 Kuma idan ya jũya sai ya yi gaggawa a cikin ƙasa dõmin ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya halaka shũka da 'ya'yan dabbõbi. Kuma Allah bã Ya son ɓarna.
2:206 Kuma idan an ce masa: "Ka ji tsõron Allah," sai girman kai da yin zunubi ya ɗauke shi To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma haƙĩƙa, shimfiɗa tã munana.
2:207 Kuma akwai daga mutãne[1] wanda yake sayar da ransa, dõmin nẽman yardar Allah: KumaAllah Mai tausayi ga bãyi ne.
2:208 Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku shiga cikin Musulunci gabã ɗaya; kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan; lalle ne shĩ a gare ku maƙiyine, bayyanan ne.
2:209 To, idan kun karkace daga bayan hujjõji bayyanannu sun zo muku to ku sani cẽwa lalle ne Allah, Mabuwãyi ne, Mai hikima.
2:210 Shin suna jira, fãce dai Allah Ya je musu a cikin wasu inuwõyi na girgije, da malã'iku, kuma an hukunta al'amarin? Kuma zuwa ga Allah al'amurra ake mayar da su.