>

Abubakar Mahmoud Gumi — 319

20:99 Kamar wancan ne Muke lãbartãwa[1] a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gun Mu.

20:100 Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanã ɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma.

20:101 Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma.

20:102 A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu.

20:103 Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma."

20:104 Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda."

20:105 Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu[1] sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa,

20:106 Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi.

20:107 "Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu."

20:108 A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya.

20:109 A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da ya yi magana[1]

20:110 Yanã sanin[1] abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani.

20:111 Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye, Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe.

20:112 Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa.

20:113 Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa.