Abubakar Mahmoud Gumi — 315
20:52 Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa."
20:53 "Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi[1] Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam.
20:54 Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali.
20:55 Daga gare ta[1] Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam.
20:56 Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyin Mu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya!
20:57 Ya ce: "Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã?"
20:58 "To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa."
20:59 Ya ce: "Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi."
20:60 Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo.
20:61 Mũsã ya ce musu, "Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe."
20:62 Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãnin su kuma suka asirta gãnawa.
20:63 Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku[1] game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya."
20:64 "Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta."