>

Abubakar Mahmoud Gumi — 313

20:13 "Kuma Nĩ nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi."

20:14 "Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni."

20:15 "Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa."

20:16 "Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka."

20:17 "Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!"

20:18 Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci[1] na dabam a gare ta."

20:19 Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!"

20:20 Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa.

20:21 Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko."

20:22 "Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam."

20:23 "Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyin Mu manya."

20:24 "Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)."

20:25 Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa[1] mini, ƙirjĩna.

20:26 kuma ka sawwake mun Al'amari na

20:27 "Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna."

20:28 "Su fahimci maganãta."

20:29 "Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena."

20:30 "Hãrũna ɗan uwana."

20:31 "Ka ƙarfafa halittata da shi."

20:32 "Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina."

20:33 "Dõmin mu tsarkake Ka da yawa."

20:34 "Kuma mu tuna Ka da yawa."

20:35 "Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu."

20:36 Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã!"

20:37 "Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam."