>

Abubakar Mahmoud Gumi — 311

19:77 Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya?"

19:78 Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?

19:79 Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa.

19:80 Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai.

19:81 Kuma suka riƙi gumãka,[1] baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.

19:82 Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu.

19:83 Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu[1] a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa?

19:84 Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar Ajali ne kawai, ƙidãyãwa.

19:85 A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma.

19:86 Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa.

19:87 Ba su malakar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama.

19:88 Kuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã!"

19:89 Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni.

19:90 Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu.

19:91 Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama.

19:92 Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã.

19:93 Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã.

19:94 Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya.

19:95 Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai.