>

Abubakar Mahmoud Gumi — 307

19:26 "Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki[1]. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."

19:27 Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!

19:28 "Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba."

19:29 Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?"

19:30 Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."[1]

19:31 "Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai."

19:32 "Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri."

19:33 "Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai."

19:34 Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.

19:35 Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã[1]. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.

19:36 "Kuma lalle Allah ne Ubangijina[1] kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."

19:37 Sai ƙungiyõyin[1] suka sãɓã wa jũna a tsakãnins u. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.

19:38 Mẽne ne ya yi jinsu[1], kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna.