>

Abubakar Mahmoud Gumi — 304

18:98 Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin[1] Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce."

18:99 Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan, yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin ƙaho sai muka tãra su, tãrãwa.[1]

18:100 Kuma Muka gitta Jahannama, a rãnar nan ga kãfirai gittãwa.

18:101 Waɗanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunã[1] Ni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa.

18:102 Shin fa, waɗanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bãyĩNa[1], majiɓinta baic iNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai.

18:103 Ka ce: "Kõ mu gaya muku game da mafĩfita hasãra ga ayyuka?"

18:104 "Waɗanda aikinsu ya ɓace a cikin rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sunã zaton lalle ne sũ, sunã kyautata, (abin da suke gani) aikin ƙwarai?"

18:105 Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓãci. Sabõda haka bã zã Mu tsayar musu da awo[1] ba a Rãnar ¡iyãma.

18:106 Wancan ne sakamakonsu shĩ ne Jahannama, sabõda kãfircinsu, kuma suka riƙi ãyõyi Na da Manzanni Na abin izgili.

18:107 Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyãfa a gare su.

18:108 Suna madawwama a cikinta, bã su nẽman makarkata daga barinta.

18:109 Ka ce: "Dã tẽku[1] ta kasance tawada ga (rubũtun) kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ta ƙãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su ƙãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin ƙari."

18:110 Ka ce: "Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa."[1]