>

Abubakar Mahmoud Gumi — 291

17:87 Fãce da rahama daga Ubangijinka. Lalle ne falalarSa ta kasance mai girma a kanka.

17:88 Ka ce: "Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance, mataimaki ga sãshi."

17:89 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun caccanza dõmin mutãne, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli sai mafi yawan mutãne suka ƙi (kõme) fãce kãfirci,

17:90 Kuma suka ce: "Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka sai kã ɓuɓɓugar[1] da idan ruwa daga ƙasa.

17:91 "Kõ kuma wata gõna daga dabĩnai da inabi ta kasance a gare ka. Sa'an nan ka ɓuɓɓugar da ƙõramu a tsakãninta ɓuɓɓugarwa."

17:92 "Kõ kuwa ka kãyar da sama a kanmu kaɓukka kõ kuwa ka zo da Allah, da malã'iku banga-banga."

17:93 "Kõ kuwa wani gida na zĩnãriya ya kasance a gare ka, kõ kuwa ka tãka a cikin sama. Kuma bã zã mu yi ĩmãni ba ga tãkawarka, sai ka sassaukõ da wani littãfi a kanmu, munã karantã shi." Ka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijĩna! Ban kasance ba fãce mutum, Manzo."

17:94 Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni, a lõkacin da shiriya ta jẽ musu, fãce sunce, "Shin, Allah zai aiko mutum ya zamo yana Manzo."

17:95 Ka ce: "Dã malã'iku sun kasance a cikin ƙasa, kuma sunã tafiya, sunã masu natsuwa, lalle ne dã mun saukar da malã'ika daga sama ya zama manzo a kansu."

17:96 Ka ce: "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da ku. Lalle Shi Ya kasance ga bãyinsa, mai ƙididdigewa ne Mai gani."