Abubakar Mahmoud Gumi — 283
17:8 Akwai tsammãnin Ubangijinku Ya yi muku rahama. Kuma idan kun sãke Mu sãke. Kuma Mun sanya Jahannama matsara ga kãfirai.
17:9 Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita[1] kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) "Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma."
17:10 Kuma lalle ne, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, Mun yimusu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
17:11 Kuma mutum yanã[1] yin addu'a da sharri kamar addu'arsa da alhẽri, kuma mutum ya kasance mai gaggãwa.
17:12 Kuma Mun sanya dare da rãna, ãyõyi biyu, sa'an nan Muka shãfe ãyar dare, kuma Muka sanya ãyar rãna mai sanyãwa a yi gani, dõmin ku nẽmi falala daga Ubangijinku, kuma dõmin ku san ƙidãyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kõme Mun bayyana shi daki-dakin bayyanãwa.
17:13 Kuma kõwane mutum Mun lazimta masa abin rekõdinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Rãnar ¡iyãma da littãfi wanda zai haɗu da shi buɗaɗɗe.
17:14 "Karanta Littãfinka. Ranka ya isa ya zama mai hisãbi a kanka a yau."
17:15 Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dõminkansa kawai kuma wanda ya ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bã ya ɗaukar nauyin wani ran, kuma ba Mu zama mãsu yin azãba ba, sai Mun aika wani Manzo.
17:16 Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta, har su yi fasadi a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa.
17:17 Kuma da yawa Muka halakar da al'ummomi a bãyan Nũhu. Kuma Ubangijinka Ya isa ya zama Mai ƙididdigewa ga zunubban bãyinSa, Mai gani.