>

Abubakar Mahmoud Gumi — 267

15:91 Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.

15:92 To, rantsuwa da Ubangijinka![1] Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.

15:93 Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.

15:94 Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.

15:95 Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu[1] izgili.

15:96 Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.

15:97 Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).

15:98 Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.

15:99 Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.

16:1 Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.

16:2 Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi[1] daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa.

16:3 Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka.

16:4 Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya.

16:5 Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci.

16:6 Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã.