Abubakar Mahmoud Gumi — 266
15:71 Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna[1] idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
15:72 Rantsuwa da[1] rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.
15:73 Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.
15:74 Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.
15:75 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.
15:76 Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.[1]
15:77 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.
15:78 Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika[1] sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!
15:79 Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.
15:80 Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri[1] sun ƙaryata Manzanni.
15:81 Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.
15:82 Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.
15:83 Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga Asuba.
15:84 Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.
15:85 Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.
15:86 Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.
15:87 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu[1] da Alƙur'ãni mai girma.
15:88 Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.
15:89 Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyanan ne."
15:90 Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,[1]