Abubakar Mahmoud Gumi — 265
15:52 A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."
15:53 Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."
15:54 Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra[1] ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"
15:55 Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."
15:56 Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijin sa, fãce ɓatattu?"
15:57 Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!"
15:58 Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."
15:59 "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."
15:60 "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."
15:61 To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,
15:62 Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."
15:63 Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."
15:64 "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."
15:65 "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."
15:66 Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga Asuba.
15:67 Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.
15:68 Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."
15:69 "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."
15:70 Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"