>

Abubakar Mahmoud Gumi — 264

15:32 Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"

15:33 Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."

15:34 Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."

15:35 "Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."

15:36 Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."

15:37 Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."

15:38 "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sanan ne."

15:39 Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."

15:40 "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."

15:41 Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."

15:42 "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."

15:43 Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya.

15:44 Tanã da ƙõfõfi bakwai,[1] ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.

15:45 Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.

15:46 "Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."

15:47 Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.

15:48 Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikin ta ba.

15:49 Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.

15:50 Kuma azãbãTa ita ce Azãba mai raɗaɗi.

15:51 Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.