Abubakar Mahmoud Gumi — 263
15:16 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.
15:17 Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.
15:18 Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.
15:19 Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.
15:20 Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã[1] da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.
15:21 Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.
15:22 Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.
15:23 Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.
15:24 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.
15:25 Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.
15:26 Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.
15:27 Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar[1] iskar zafi.
15:28 Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."
15:29 "To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa[1] a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."
15:30 Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.
15:31 Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.