>

Abubakar Mahmoud Gumi — 262

15:1 A. L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.

15:2 Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.[1]

15:3 Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.

15:4 Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.

15:5 Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.

15:6 Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."

15:7 "Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"

15:8 Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,[1] bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.

15:9 Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.

15:10 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka.

15:11 Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.

15:12 Kamar wancan ne Muke shigar da shi[1] a cikin zukãtan mãsu laifi.

15:13 Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige[1] .

15:14 Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.

15:15 Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."