Abubakar Mahmoud Gumi — 25
2:164 Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa, da sãɓãwar dare da yini, da jirãge wadaɗnda suke gudana a cikin tẽku (ɗauke) da abin da yake amfãnin mutãne, da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta, kuma Ya wãtsa, a cikinta, daga dukan dabba, kuma da jũyãwar iskõki da girgije hõrarre a tsakãnin sama da ƙasa; haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.
2:165 Kuma akwai daga mutãne wanda yake riƙon kinãye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma waɗanda suka yi ĩmãni ne mafiya tsananin so[1] ga Allah. Kuma dã waɗanda[2] suka yi zãlunci, suna ganin lõkacin da zã su ga azãba, da cewa lalle ne ƙarfi ga Allah yake duka, da cẽwa lalle neAllah Mai tsananin azãba ne.
2:166 A lõkacin da waɗanda aka bi suka barranta daga waɗanda suka bi, kuma suka ga azãba, kuma sabubba suka yanke da su.
2:167 Kuma waɗanda suka bi, suka ce: "Dã lalle ne muna da wata kõmãwa (dũniya) sai mu barranta dagagare su kamar yadda suka barranta daga gare mu (dã ba su riƙi kinãyen ba)." Kamar wancan ne Allah ke nũna musu ayyukansu, suna da nadãmõmi a kansu, kuma ba su zama mãsu fita daga wutar ba.
2:168 Yã ku mutãne![1] Ku ci daga abin da yake a cikin ƙasa, wanda yake halal, mai dãɗi. Kuma kada ku bi zambiyõyin[2] Shaiɗan. Lalle ne shi, gare ku, maƙiyi ne bayyananne.
2:169 Yana umurnin ku ne kawai da mugun aiki da alfãsha, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba ga Allah.