>

Abubakar Mahmoud Gumi — 241

12:44 Suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yãye-yãyen mafarki ba."

12:45 Kuma wannan da ya kuɓuta daga cikinsu ya ce: a bãyan yã yi tunãni a lõkaci mai tsawo, "Nĩ, inã bã ku lãbãri game da fassararsa. Sai ku aike ni."

12:46 "Yã Yũsufu! Yã kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shãnu bakwai mãsu ƙiba, waɗansu bakwai rãmammu sunã cin su, da zangarku bakwai kõrãye da waɗansu ƙẽƙasassu, tsammãnĩna in kõma ga mutãne, tsammãninsu zã su sani."

12:47 Ya ce: "Kunã shũka, shẽkara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa,[1] sai kaɗan daga abin da kuke ci."

12:48 "Sa'an nan kuma waɗansu bakwai mãsu tsanani su zo daga hãyan wancan, su cinye abin da kuka gabãtar dõminsu, fãce kaɗan daga abin da kuke ãdanãwa."

12:49 "Sa'an nan kuma wata shẽkara ta zo daga bãyan wancan, a cikinta ake yi wa mutãne ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke mãtsar abin sha."

12:50 Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi." To, a lõkacin da manzo ya je masa (Yũsufu), ya ce: "Ka kõma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Mẽnene hãlin mãtãyen nan waɗanda suka yanyanke hannãyensu? Lalle ne Ubangijĩna ne Masani game da kaidin su."

12:51 Ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinku, a lõkacin da kaka nẽmi Yũsufu daga kansa?" Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummũnan aiki a kansaba." Mãtar Azĩz ta ce: "Yanzu fagaskiya[1] ta bayyana. Nĩ ce nã nẽme shi daga kansa. Kuma lalle ne shĩ, haƙĩƙa, yanã daga mãsu gaskiya.

12:52 "Wancan ne, dõmin ya san cẽwa lalle ne ni ban yaudareshi ba a ɓõye, kuma lalle Allah bã Ya shiryar da kaidin mayaudara."