>

Abubakar Mahmoud Gumi — 236

12:5 Ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne.[1]

12:6 "Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima."

12:7 Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi[1] sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa[2] dõmin mãsu tambaya.

12:8 A lõkacin da suka ce:[1] lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.

12:9 Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai.

12:10 Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."

12:11 Suka ce: "Yã bãbanmu[1]! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi?"

12:12 "Ka bar shi tãre da mu a gõbe, ya ji dãɗi, kuma ya yi wãsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, mãsu tsaro ne."

12:13 Ya ce: "Lalle ne ni, haƙãƙa yanã ɓãta mini rai ku tafii da shi, Kuma inã tsõron kerkẽci ya cinye shi, alhãli ku kuwa kunã mãsu shagala daga gare shi."

12:14 Suka ce: "Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhãli kuwa munã dangin jũna, lalle ne mũ, a sa'an nan, hakĩka, mun zama mãsu hasãra."