>

Abubakar Mahmoud Gumi — 235

11:118 Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã Yã sanya mutãne al'umma guda. Kuma bã zã su gushe ba sunã mãsu sãɓã wa jũna.

11:119 Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama, kuma dõmin wannan[1] ne Ya halicce su. Kuma kalmar "Ubangijinka" Lalle ne zã Ni cika Jahannama da aljannu da mutãne gaba ɗaya" ta cika.

11:120 Kuma dũbi dai Munã bã da lãbãri a gare ka daga lãbarun Manzanni, abin da Muke tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan da wa'azi da tunãtarwã ga mãsu ĩmãni.

11:121 kuma kace wa waɗanda bã su yin ĩmãni, "Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle mũ mãsu aiki ne.

11:122 "Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko[1] ne."

11:123 Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake. Kuma zuwa gare Shi ake mayar da dukan al'amari. Sabõda haka ku bauta Masa kuma ku dõgara a kanSa. Kuma Ubangijinka bai zama Mai gafala daga abin da kuke aikatãwa ba.

12:1 A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne.

12:2 Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta.

12:3 Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga gafalallu.

12:4 A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni."