>

Abubakar Mahmoud Gumi — 234

11:109 Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma haƙĩƙa Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba.

11:110 Kuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãɓã[1] wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma haƙĩƙa, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto.

11:111 Kuma lalle, haƙĩƙa, Ubangijinka Mai cika wa kõwa (sakamakon) Ayyukan sa ne. Lalle Shĩ, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke aikatãwa.

11:112 Sai ka daidaitu[1] kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.

11:113 Kada ku karkata[1] zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba.

11:114 Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. Wancan[1] ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.

11:115 Kuma ka yi haƙuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa.[1]

11:116 To, don me mãsu hankali ba su kasance daga mutãnen ƙarnõnin da suke a gabãninku ba, sunã hani daga ɓarna a cikin ƙasa? fãce kaɗan daga wanda Muka kuɓutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma waɗanda suka yi zãlunci suka bin abin da aka ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance mãsu laifi.

11:117 Kuma Ubangijinka bai kasance Yanã halakar da alƙaryu sabõda wani zãlunci ba, alhãli mutãnensu sunã mãsu gyãrãwa.[1]