Abubakar Mahmoud Gumi — 233
11:98 Yanã shũgabantar mutãnensa a Rãnar Kiyãma, har ya tuzgar da su a wuta. Kuma tir da irin tuzgãwar su.
11:99 Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. Tir da kyautar[1] da ake yi musu.
11:100 Wancan Yanã daga lãbãran alƙaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe.[1]
11:101 Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun zãlunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawar su waɗan da suke kiran su, baicin Allah, ba su wadãtar musu kõme ba a lõkacin da umurnin Ubangijin ka ya je, kuma (gumãkan) ba su ƙãra musu wani abu ba fãce hasãra.
11:102 Kuma kamar wancan ne kãmun Ubangijin ka, idan Ya kãma alƙaryõyi alhãli kuwa sunã mãsu zãlunci. Lalle kamũn Sa mai raɗaɗi ne, mai tsanani.
11:103 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga wanda ya ji tsõron azãbar Lãhira. Wancan yini ne wanda ake tãra mutãne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta.
11:104 Ba Mu jinkirtã shi ba fãce dõmin ajali ƙidãyayye.
11:105 Rãnar da za ta zo wani rai ba ya iya magana fãce da izninSa. Sa'an nan daga cikinsu akwai shaƙiyyi da mai Arziki.
11:106 To, amma waɗan da suka yi shaƙãwa, to, sunã a cikin wuta. Sunã mãsu ƙãra da shẽka a cikinta.
11:107 Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatãwa ne ga abin da Yake nufi.
11:108 Amma waɗan da suka yi arziki to, sunã a cikin Aljanna sunã madawwama, a cikinta, matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda bã ta yankẽwa.